Kadarorin gwamnati: Za'a a fara sauraron bahasi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Majalisar Dokokin Najeriya

A Najeriya, a ranar litinin ne wani kwamitin da Majalisar Dattawan Kasar ta kafa zai fara sauraron ra`ayin jama`a a kan makomar wasu kadarorin gwamnati da aka sayar.

Kwamitin dai ya shirya sauraron ra`ayoyin jama`a ne a ci gaba da binciken da yake yi game abin da ya hana mafi yawan wasu kamfanoni ci gaba da aiki bayan an sayar da su.

Sai dai wasu `yan kasar na zargin cewa an kafa kwamitin ne da nufin yi wa wasu bi-ta-da-kulli, amma kwamitin ya musanta hakan.

Kimanin kamfanoni dari biyu Majalisar Dattawan ta ce za ta bi kadin yadda aka siyar da su.

Kamfanoni sun durkushe

Kuma binciken zai fara ne da matakin Hukumar da ke kula da alhakin siyarda kadarorin.

Senata Ahmad Lawal wanda shine shugaban kwamitin binciken ya ce; " Gaskiya labarin da muka samu shine yawancin kamfanoni da aka siyar ba sa aiki."

"Ya dace akwai tsare tsaren da ya kamata abi a lokacin da aka siyar da su domin a inganta su, ba wai su durkushe ba." In ji Senata Ahmad Lawal.

Binciken dai zai shafi wasu daga cikin kamfanonin da aka siyar a lokacin gwamnatin Cif Olusegun Obasanjo.