Saudiyya ta janye Jakadanta a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Sarki Abdallah

Sarki Abdullah na kasar Saudiyya ya ce, tashin hankalinda gwamnatin Syria ke amfani da shi akan alummar kasar ba za a lamunce masa ba.

A wata sanarwarsa da kafar talabijin na al-Arabiya ta fitar, sarkin ya ce dole ne gwamnatin Syria ta aiwatar da sauye sauye na hakika ta kuma dakatar da abinda ya kira naurorin kashe kashe, kafin alamarin ya lalace.

A karon farko dai, kungiyar kasashen Larabawa ta yi suka dangane da kashe kashen da ake yi a Syria a hukumance.

Sarkin dai ya yi kira ga gwamnatin kasar ta Syria da daina kashe al'umarta da ke neman sauyi, inda kuma ya bukaci kasar da ta gudanar da sauye-sauyen inganta rayuwar al'ummar kasar.

Sarki Abdallah ya ce kasar Saudiya ba ta amince da abun dake faruwa ba a Syria, ko kadan, domin haka Syria ta gaggauta neman yadda za ta magance rikicin siyasar kasar cikin lalama, ko kuma ta gamu da fushin ta.

Jawabin Sarki Abdallah na zuwa ne a ranar da rahotanni su ka ce sojojin Syria sun kashe akalla masu zanga zanga hamsin.

Wannan dai wani babban sauyi ne aka samu kan harkar diplomasiyyar kasar Saudiya na kin tsoma baki a kan rikicin na Syria.

A yanzu haka dai Shugaba Assad na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya.