Saudiyya ta yiwa Syria kakkausan suka

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sarki Abdalla na Saudiyya

Kasar Saudiyya ta yi kakkausan suka ga kasar Syria game da matakan da ta ke dauka na murkushe masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati. Hakazalika kasat ta Saudiyya ta dauki matakin janye jakadanta daga kasar Syriyan. Kasar Turkiyya ma ta yi irin wannan kakkausan suka, yayinda kungiyar hadin kan larabawa, ma ta nemi da a dakatar da zubar da jini nan take. Ba kasafai ne dai kasar Saudiyya ke fitowa ta soki wata kasar Larabawa ba. Sheikh Usman Bari wani masanin diplomasiyya ne dan kasar Ghana, kuma ya shaidawa BBC cewa wannan suka na Saudiyya yazo da mamali.