Gidan Talabijin na Syria ya ce soji za su janye daga Hama

Masu zanga zanga a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zanga a Syria

Gidan Telbijin na Syria ya ce dakarun Sojin kasar sun fara ficewa daga garin Hama.

Gidan Telbijin din yace Sojojin kasar sun kammala aikinsu kuma an fara samun kwanciyar hanakali a garin.

A kwanakin baya ne dakarun tsaro suka farma garin, abun da ya ruruta wutar tashin hankalin da aka yi fama dashi a yunkurin shawo kan masu zanga zanga.

'yan kasar dadama ne dai aka hallaka a tashin hankalin

Sakatare Janar na kungiyar kasashen larabawa Nabil Al'araby ya nuna damuwa akan abunda ke faruwa a Syria. Wasu kasashen larabawa sun bi sahun sauran kasashe, wajen yin TIR da yadda gwamnatin Syria ke amfani da karfin tsiya a kan masu zanga zanga.

Kuwait ta janye jakadanta a Syria, haka ma Bahrain, kuma kafin su, saudiyya ma ta janye nata jakadan daga kasar.

A misra, majalisar kula da harkar addinin musulunci mafi daraja ta Al-azhar, ta fidda wata sanarwa da ke kira ga gwamnatin Syria data gaggauta kawo karshen zubad da jinin da ake yi