Tarzoma na ci gaba da yaduwa a Burtaniya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fiye da mutane dari biyu ne aka kama

A daren ranar litinin ne dai aka shiga rana ta uku da tarzoma ta barke a birnin Ladan yayinda kuma ake a ci gaba da dibar ganima a wurare da dama a birnin.

Ana dai cinnawa gine-gine wuta a Peckham da Croydon a kudancin birnin da Ealing a yammacin birnin da kuma Hackney dake gabashin birnin.

Wakiliyar BBC tace hutunan telbijin daga unguwar Hackney dake gabashin London, sun nuno yadda 'yansanda ke karawa da matasa sanye da riga mai hula.

Fiye da mutane dari biyu ne aka ce an kama a hargitsin. Tarzomar har wa yau ta fara yaduwa zuwa biranen Birmingham da Liverpool da kuma Bristol a yayinda 'yan sanda suka cafke mutane da dama.

Pira Ministan Burtaniya, David Cameron ya katse hutun da yake yi a Italiya inda ya dawo gida domin shawo kan lamarin.

Rikicin ya samo asali ne a anguwar Tottenham a arewacin London ranar Asabar, bayan wata zanga zangar lumana game da kisan wani mutum.