An zargi gwamnatin Zimbabwe da azabtar da fursunoni

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe

Shaidu na ci gaba da bayyana dake nuna cewa, dakarun kasar Zimbabwe na amfani da wasu sansanin hakar lu'lu' ta Marange domin azabtar da mutane.

Wakiliyar BBC ta ce, fursunonin da aka sako baya bayan nan sun ce ana yi masu dukan tsiya sau da dama a ko wacce rana, wani lokacin a tafin kafarsu.

Sun ce fyade akai akai ake yiwa mata, ga karancin abinci, kuma wasu ma ba sa iya tafiya idan aka sako su.

Fursunoni guda biyu sun ce an cuna masu karnuka, suka yayyaga su.

Yawancin wadanda ke sansanonin dai na hakar lu'lu'n ne ta haramtacciyar hanya.

Izuwa yanzu gwamnatin Zimbabwe ba ta maida martani kan wadannan zarge zarge na BBC ba.