Shugaban Nijar ya kai ziyara Najeria

Shugaba Mahamadou Issoufou
Image caption Shugaba Mahamadou Issoufou

Najeriya da Jumhuriyar Niger sun amince za su duba yiwuwar kyautata harkar sufuri a tsakaninsu ta yadda harkar kasuwanci da tattalin arzikinsu za su bunkasa.

Kasashe biyun sun kuduri wannan aniyar ne a wata tattaunawar da shugabanninsu suka yi, lokacin wata ziyarar da shugaban jumhuriyar Niger, Alhaji Muhammadu Issoufou ya kai Nigeria a yau talata.

Dukkan shugabannin dai sun yarda za su gina hanyoyin mota da na jirgin kasa a kan iyakokinsu mai tsawon kilomita dubu daya da dari biyar.

Wannan dai ita ce ziyarar aiki ta farko da shugaban Nijar din yake kaiwa Najeria tun bayan hawansa kan karagar mulki a cikin watan Afrilun da ya gabata.