Syria na fuskantar karin matsin lamba

Ministan harkokin wajen Turkiyya Ahmet Davotoglu ya isa Damascus, babban birnin Syria don yin kira da aka kawo karshen yin amfani da karfin soji a kan masu zanga zanga.

An ruwaito cewa tankokin yakin Syria sun kutsa garin Bannish dake kusa da iya da Turkiyya.

Kasashen Larabawa da dama ne suka janye jakadunsu daga Syria.

Babban Jami'in majalisar dinkin Duniya akan kashe kashen gilla, Christof Heyns ya yi maraba da yadda Syriyar ke shan matsin lamba.