An yi watsi da tuhumar da ake yiwa Dr Besigye a Uganda

Dr Kiiza Besigye Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dr Kiiza Besigye

Wata kotu a Uganda ta yi watsi da tuhumar da ake yiwa jagoran 'yan adawan kasar, Dr Kiiza Besigye.

A farkon wannan shekarar dai aka kama Dr Besigye sau da dama bisa zargin kasancewa da hannu a jerin zanga-zangar da aka gudanar na nuna adawa da gwamnatin kasar ta Uganda.

Alkalin kotun, George Watye-kere ya amince da bukatar lawoyoyin Dr Besigye cewa masu shigar da kara sun gaza gabatar da wata kwakwarar hujja akan shi, saboda haka ya yi watsi da karar.

A cikin watan Afrilun da ya gabata ne dai, Dr Besigye tare da wasu magoya bayansa ya halarci wasu jerin zanga-zanga da aka yiwa lakabi da tafiya aiki da kafa. Manufar zanga-zangar, wadda aka rika yi sau 2 a mako, ita ce kawo gwamnatin kasar ta rage tsadar rayuwa.