An sako uku daga Malaman da aka kama a Biu

Jami'an 'yan sanda a Nijeriya
Image caption Jami'an 'yan sanda a Nijeriya

Rahotanni daga garin Biu a kudancin jihar Borno ta Nijeriya sun ce rundunar Sojoji ta 23 ta sako uku daga cikin malaman makarantar Jihadil Islam bakwai da ta cafke bisa zargin cewar 'ya'yan kungiyar nan ce ta Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram.

Cafke wadannan malamai dai ya haifar da wata mummunar tarzoma tsakanin jami'an sojin da wasu gungun matasa da 'yan makarantar Islamiyyar wanda yayi sanadiyyar rasuwar wata mata mai goyo tare da jikkata wasu, bayan da jami'an sojin suka bude wuta.

Kawo yanzu dai Rundunar Sojin ta 23 din dake Yola na jihar Adamawa wadda sojojin na garin Biu ke karkashinta ba ta yi wani cikakken bayani ba game da cafke wadannan malamai.