Gaddafi ya zargi NATO da kashe farar hula

Shugaban Libya Kanar Muammar Gaddafi, ya aikewa mambobin kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya wasika, da a ciki ya dora masu alhakin kisan farar hula da dakarun tsaron NATO suka yi a kasar.

Gidan Telbijin din Libya ya ce Gaddafi ya aikewa shugabannin kasashe 15 dake da wakilci a kwamitin wasika, yana cewa su ne ke da alhakin wani hari ta sama akan wani kauye, a jiya, da ya hallaka fararen hula 85.

Hukumomin Libya sun ce an hari garin ne don bai wa 'yan tawaye damar kama shi.