Nigeria da Niger sun kudiri aniyar inganta noma

Image caption Shugaban kasar Nijer

Najeriya da makwabciyarta jamhuriyar Niger sun kudiri aniyar inganta harkokin noma da kasuwanci ta hanyar samar da ingantaccen tsarin sufuri a tsakanin kasashen biyu.

Yaki da ta`addanci ma dai na daga cikin batutuwan da Shugabannin kasashe biyun suka cimma matsaya akai a lokacin da shugaban jumhuriyar Niger din ya kai ziyara Najeriya.

Mallam Bazum Mohammed shi ne ministan harkokin wajen jamhuriyar Niger ya shaidawa BBC cewa kasashen biyu zasu aiki tare wurin samar da horaswa ga jami'an tsaro ta yadda zasu iya tunkarar ta'adanci.

A jiya ne dai shugaban kasan Nijer Mahamodou Isoufou ya tattauna da shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya