Ana taro kan kare al'ummar Nijer daga illar makamakshi

Image caption Shugaban Nijer Muhammadou Issoufou

A jamhuriyar Nijar yau an shiga kwana na na biyu na wani taron kara wa juna sani da gwamnatin kasar ta shirya tare da hadin gwiwar hukumar makamashin nukliya ta duniya AIEA. Makasudin taron dai shi ne taimaka wa kasar ta Nijar wajen samar da matakan kare al'umarta daga duk wasu illoli ko hadurran da ke tattare da makamashin nukliya da sinadiran da ake sarrafa shi da su. A cikin watan mayu na 2010 ne gwamnatin ta Nijar ta yi wani taro da hukumar makamashin nukliyar ta duniya a Yamai inda bangarorin biyu suka amince da wani shiri na bayar da horo ga duk wasu jami'an da ke mu'amula da makamashin nukliya, domin su san illolin da ke tattare da shi da kuma matakan da ya kamata a dauka domin tunkarar matsala idan ta taso.