Kasuwar hannayen jari ta yi warwas a Turai

Darajar hannayen jari a turai ta yi kasa warwas, kuma hannayen jarin bankuna ne suka fi jin jiki. Rade-radin cewa Faransa zata rasa darajarta ta daya a kimar masu karbar bashi sun sa karfin hannayen jarin bankunan kasar sun yi kasa. Amma kuma hukumomin kasar sunce suna aiki tukuru wajen kawo daidaito a tattalin arzikin kasar.