Za mu dauki tsauraran matakai - Cameron

david cameron Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Libya ta nemi Cameron da ya sauka bayan da ta ce ya gaza

Fira ministan Burtaniya David Cameron, ya ce za a kara girke 'yan sanda a titunan biranen kasar domin kawar da tarzomar da ke faruwa a kasar.

Ya kuma yi alkawarin 'yan sanda za su samu duk kayan aiki da goyon bayan da suke samu - domin daukar duk matakan da suke ganin sun dace.

"Ba za mu lamunce da ci gaba da wannan tarzoma ba, kuma za a kawo karshenta," a cewarsa.

"Kawo yanzu an kama fiye da mutane 700 a birnin London kawai. Za mu samar musu da duk kayan da suke bukata ciki harda tankokin ruwa idan ta kama.

Yana magana ne bayan da ya jagoranci wani taron kwamitin tsaro na gaggawa a fadar gwamnati.

Fira Ministan ya ce halayyar da masu tarzomar suka nuna ciki harda yara kanana ta nuna cewa wasu al'ummar Burtaniya na da matsalar tarbiyya.

Ya yi alkawarin cewa gwamnati ba za ta bar wasu tsiraru su jefa tsoro a cikin zukatan jama'a ba.

An soki jami'an 'yan sanda

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Biranen da tarzomar ta shafa a ranar 9 ga watan Agusta

Ko da yake abubuwa sun dan lafa a akasarin birnin Landan, a dare na hudu an ci gaba da fasa shaguna ko banka musu wuta da kuma dibar ganima a wasu yankunan a birnin Manchester da Liverpool da kuma Birmingham.

An kuma ci gaba da suka a kan matakan da 'yan sanda ke dauka, wadanda 'yan siyasa da ma jama'ar gari ke cewa ba su wadatar ba.

Sai dai wani babban jami'in rundunar 'yan sanda ta Manchester ya ce jami'ansa sun fuskanci tashin hankali mara misaltuwa yayin da suke fafatawa da wasu bata gari wadanda ke kokarin ta da zaune tsaye.

Wani mai fafutuka a Manchester, Muhammad Shafiq, ya shaidawa BBC cewa ya ga matasa kusan dubu biyu suna dauki ba dadi da 'yan sanda.

"Mun ga gungun bata gari marasa tunani suna farfasa shaguna, suna kuma jifan 'yan sanda da duwatsu. Irin wannan dabi'a ba ta cancanta ba sam".

Karin bayani