A yau za'a kaddamar da Majalisar dokokin ECOWAS

Image caption Shugabannin Kasashen kungiyar ECOWAS

A Najeriya, a yau ne ake kaddamar da Majalisar dokokin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS ko CEDAO.

Wannan dai ita ce jamhuriya ta uku tun kafuwar majalisar a shekarar 2000.

Rawar da majalisar dai ke takawa ba ta wuce ta ba da shawararwari ga majalisar zartarwar kungiyar ba, koda yake wasu na ganin cewa kamata ya yi a karfafa majalisar ta yadda dokokinta za su yi tasiri a kan kasashen da ke cikin kungiyar baki daya.

Sai dai wasu na ganin cewa dokokin da take yi sun fara amfanar shiyyar ta hanyar baiwa membobin damar zuwa wata kasa dake yankin ba tare neman izinin shiga ba.

Senata Muhammed Ali Ndume ya kuma ce Majalisar na kokarin ganin yankin ya fara amfanin da kudin na bai daya irin na tarayar Turai