Fashi a teku na karuwa a yankin ruwan Benin

Jirgin ruwa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jirgin ruwa

Hukumar da ke kula da zirga zirgar jiragen ruwa ta ce, fashi a teku na kara zama ruwan dare a yankin ruwayen kasar Benin, a yammacin Afirka, inda a watanni shidda na farkon wannan shekarar, aka kai hare-hare kimanin goma sha biyar.

Shugaban hukumar, Kyaftin Pottengal Mukundan ya shaidawa BBC cewa, a yawancin lokuta 'yan fashin na kai jirgin ruwan da suka kama, mai dakon mai, zuwa wani yankin na dabam, inda suke tsiyaye man a cikin wani jirgin da ke tsaye yana jira.

Ya ce, galibi 'yan fashin na sakin ma'aikatan jirgin ruwan ba tare da sun nemi kudaden fansa ba - ko da yake a lokuta da dama suna taba lafiyarsu.