Rashin tabbas a kasuwannin kudi na duniya

Rashin tabbas a kasuwannin kudi na duniya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zuba jari na cikin halin dar-dar

An ci gaba da fuskantar rashin tabbas a kasuwannin hada-hadar hannayen jari na duniya, bayan da darajar hannayen jari ta fadi a Turai da Amirka ranar Laraba.

Hannayen jarin bankunan Faransa sun sake fuskantar matsin lamba, abun da ya dusashe irin farfadowar da suka yi na wani dan lokaci tun farko.

Rububin da masu zuba jari suka yi na kwasar garabasa bayan faduwar darajar hannayen jari ranar Laraba ya sa darajar hannayen jarin ta farfado a cinikin da aka yi a farkon bude kasuwannin hada-hadar hannayen jari na Turai.

Sai dai kuma ba a jima ba sai darajar hannayen jarin ta sake karyewa saboda sabuwar fargabar da ake yi cewa bangaren harkar banki na Faransa bai da cikakkiyar lafiya.

Matsin lamba kan Faransa

Darajar jarin bankin Societe Generale ta kara faduwa warwas duk da tabbacin da shugaban bankin ya bayar cewa asusunsa cike ya ke.

Bankunan Faransa dai na rike da takardun lamuni da dama na gwamnatocin Italiya da Spaniya da Girka; faragabar da ake yi kuma ita ce idan matsalar bashin da ta dabaibaye wasu kasahen Turai ta yadu, bankunan na Faransa za su tafka mummunar asara.

A halin da ake ciki kuma, gwamnatin Faransar ma na fuskantar matsin lamba, yayin da ake ci gaba da rade-radin cewa za ta rasa matsayinta mai daraja ta daya a kimar kasashe masu karbar bashi.

Yiwuwar faruwar hakan dai ta sa cikin kasuwannin hada-hadar hannayen jari ya duri ruwa, ko da yake cibiyoyin da ke kimanta darajar kasashe masu karbar bashi sun ce ba su da niyyar rage darajar kasar ta Faransa.