Shugaban Nijer yayi alkawarin yaki da bauta

Shugaban Nijer
Image caption Shugaban Nijer

A jamhuriyar Nijar kungiyar kare hakin dan adam ta Timidria da ke yaki da bauta a kasar ta ce ta yi marhabin da aniyar da shugaban kasar Alhaji Issoufou Mahamadou ya dauka na yaki da bauta, kuma a shirye take ta kawo wa gwamnatin duk wani goyon bayan da ya dace domin cim ma nasara.

Shugaban kungiyar ta Timidria ne Malam Ibrahim Habibu ya bayyana haka a lokacin wani taron manema labarai da ya kira yau din nan a Yamai.

A makon da ya gabata ne dai shugaban kasar, Alhaji Issoufou Mahamadou a cikin jawabinsa albarkacin zagayowar shekaru 51 da Nijar ta samu 'yancin kanta, ya dauki alkawalin gwamnatinsa za ta dage wajen yaki da duk wasu matsaloli irin na keta hakkin Bil'Adama, musamman ma bauta.