Mutane biyar suka hallaka a Pakistan

Image caption Wani wuri da bam ya tashi a Peshawar

'Yansanda a Arewa maso yammacin Pakistan sun ce akalla mutane biyar suka hallaka a fashewar wani bam a Peshawar.

Sun ce anyi amfani da naura wurin tada bam kusa da wata motar 'yansanda, inda nan take yansanda hudu da wani karamin yaro suka mutu yayinda da dama suka samu raunuka.

Pashewar wanda birni ne dake kusa da yankunan kabilun Pakistan yana fama da hare-haren bama-bamai da yawanci ake kaiwa jami'an tsaro.