Mutane uku sun rasu sakamakon rikici a Filato

Jami'in dan sanda a Nijeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'in dan sanda a Nijeriya

Rahotanni daga jihar Filato a Nijeria na cewa mutane uku 'yan gida daya sun rasa rayukansu a wani sabon hari da aka kai a karamar hukumar Barikin Ladi.

Hukumomin tsaro a jihar ta Filato mai yawan fuskantar tashe-tashen hankula, sun bayyana cewa suna kan binciken lamarin da nufin gano wadanda suke da hannu.

Harin dai ya zo ne kwana biyu bayan da wasu mutanen uku suma 'yan gida daya suka rasa rayukansu kana shanu masu yawan gaske suka salwanta a wani farmaki makamancin wannan a karamarar hukumar ta Barikin Ladi.