Dubban mutane ke tsare dangane da tarzoma a London

Wani da ake zargi game da tarzomar Birtaniya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wani da ake zargi game da tarzomar Birtaniya

Fiye da mutane dubu da dari biyar ne ake tsare da su yanzu haka a sakamakon tashin hankalin da aka samu a Ingla a cikin makon nan.

Wani babban jami'in dan sanda a London yace ji mamaki mamaki idan ba a cafke wasu karin mutane dubu ba, yayinda 'yan sanda suka shiga farautar wadanda suka taka rawa a zanga zangar.

Kotuna sun yi zama har cikin dare, kuma an tsananta hukunci a kan wadanda aka samu da laifi.

An yanke wa wani mutum hukuncin daurin wata shidda a gidan yari saboda an same shi da laifin satar katan din ruwa da ake saidawa dala biyar. Wakilin bbc yace yayinda ake shara'ar wadanda ake zargin, shugabanin jama'a da matasa na duba hanyoyin hana faruwar zanga zangar a gaba.

Yawancinsu dai na ganin wadannan ba matsaloli ne sababi ba don suna nan a kasa tun da jimawa.

Tun farko dai daya daga cikin manyan jami'an 'yan sandan Birtaniya yayi fatali da sukan da ake yiwa dabarun da 'yan sandan suka yi amfani da su wajen shawo kan tashin hankalin da ya auku a sassa da dama na Ingila.

Sir Hugh Orde wanda shi ne shugaban kungiyar manyan jami'an 'yan sandan yace, kwamandojin 'yan sandan sun dau matakai cikin gaggawa a daren farko da tarzoma tayi kamari a Ingila:

Ya kuma maida martani a kan kalaman da Theresa May tayi a ranar laraba a hirar da tayi ta wayar taroho da manyan 'yan sanda inda ta umurce su akan suyi amfani da tsarin rundunar 'yan sandan na birnin landan kuma su soke shirin tafiya hutu, inda ya ce sakatariyar harkokin cikin gida ta kasar bata da ikon yin haka.

Sir Hugh yace dubarun 'yan sanda ba su da wata alaka da katse hutun Madam May da David Cameron da kuma manyan ministocin kasar.

A baya dai sir Hugh ya samu sabani da gwamnatin kasar akan matakin da taka dauka akan 'yan sanda musaman kan yan siyasar da aka zaba su rika a ido akan 'yan sanda Ingila da kuma yankin wales.

Sai dai kalamansa na baya bayanan zasu janyo shaku akan ko zai iya aiki tare da sakatariyar cikin gida ta kasar a matsayin kwamishinan rundunar yansanda na birnin landan idan ya yanke shawarar neman mukamin kenan.