Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Fitar hakoran Jarirai

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Wasu yaran kan fara hakori da wuri yayin da wasu ke samun jinkiri

Fitar hakora dai na daga cikin abubuwan da kan baiwa yara wahala a wasu lokutan, wanda har ya kan janyo jikinsu ya yi zafi, ko kuma ya haifar musu da rashin sukuni, ko yawan kuka.

A wani bincike da Hukumar Lafiya ta Burtaniya NHS ta yi akan fitar hakora, ta ce akan fara halittar hakoran jarirai ne tun suna cikin mahaifiyarsu, galibi kuma su kan fara bullowa daga dadashi da zarar yaro ya kai kimanin wattani uku zuwa shida da haihuwa.

Hukumar NHS din dai ta bayyana cewa lokutan da yaran kan yi hakori ya banbanta.

Yayin da wasu yaran akan haife su da hakora, wasu kan fara ne daga watanni uku, wasu ma har sai bayan sun shekara, amma dai galibi yara kan gama hakoran ne daga shekaru biyu zuwa biyu da rabi.

A wani bincike kuwa da sashen Lafiya na BBC ya guadanar, wasu yaran kan yi fama da zafin jiki, da rashin sukuni, da har a wasu lokutan su dinga farkawa cikin dare suna kuka a lokacin da hakoran su ke bullowa daga dadashi.

Kuma a wasu lokutan, dadashin kan yi ja, idan aka leka bakin za'a ga alamar ya dan turo har wani sa'in ya yi alamar hakori, ko kuma kumatun su dan kumbura, sannan kuma komai yaro ya dauka sai ya ruga a baki.

Sau tari dai akan dora alhakin wasu cututtukan kamar zazzabi ko mura ko gudawa ko ciwon ido da dai sauransu akan fitar hakora.

Shirin Haifi Ki Yaye na BBC Hausa na wannan makon, yana dauke da bayanai kan ababan da suka shafi fitar hakoran jarirai.