Sojin Najeriya za su gudanar da bincike a jihar Borno

Image caption Wani wuri da aka cinnawa wuta a Maiduguri

Ministan tsaron Najeriya ya bukaci rundunar sojan kasar ta gudanar da bincike dangane da zargin da ake yiwa sojan dake aikin shawo kan kalubalen tsaron da ake fuskanta a yankin arewa maso gabas na kasar.

Ministan tsaron, Bello Muhammed ya bayyana hakan ne bayan kisan wata mata ranar Laraba ya haddasa fito-na-fito tsakanin soja da wasu da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Tashin hankalin dake aukuwa musamman a jihar Barno dai ya tliastawa dubban mutane barin muhallinsu.