Yau ce ranar bikin matasa ta duniya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu matasa a jami'ar Lagos

A yau ne ake bikin ranar matasa ta duniya karo na goma sha daya da aka soma tun daga shekara ta 2000.

An dai ware wannan ranar ne dai domin baiwa gwamnatoci dama su janyo hankulan jama'a kan batutuwa da suka shafi matasa.

A fadin duniya dai ana gudanar da taruka da bitoci da gwamnatoci a matakai daban daban ke shiryawa domin wannan rana.

Galibi dai akan yi amfani da wannan ranar wajen duba halin da matasan ke ciki ,musamman gudummuwar da suke bayarwa ga ci gaban kasashensu, matsalolin da suke fuskanta, da kuma duba hanyoyin magance su.