An kashe wata mai sharia a Brazil

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugabar Kasar brazil

A birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil, an kashe wata mai shari'a wadda ta yi fice wajen yaki da gungun masu aikata miyagun laifuffuka.

Wadansu mutane wadanda suka lullube fuskar su a kan babur ne suka harbi Mai Shari'a Patricia Asioli har fiye da sau ashirin a kofar gidanta da ke birnin Niteroi.

Daga cikin wadanda marigayiyar ta taba yankewa hukunci dai har da 'yan sanda da dama wadanda suka aikata laifuffuka yayin da suke bakin aiki.

Iyalinta dai sun ce, ko da yake an sha yi mata barazana, ba ta da dan sanda mai tsaron lafiyarta.

Gwamnan Jihar Rio de Janeiro ya sha alwashin gudanar da bincike cikin hanzari kotun koli ta kasar kuma ta yi Allah-wadai da kisan tana mai cewa wannan wani hari ne a kan mulkin dimokuradiyya da dokokin kasa.