Cameron zai gana da wani tsohon jami'in tsaro

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tarzomar Birtaniya

Wani tsohon babban jami'in 'yan sandan Amurka ya amince ya gana da Firaministan Birtaniya, David Cameron a watan gobe domin ya bada shawara akan yadda za'a yaki kungiyoyin matasa masu aikata muggan laifuka a biranen Birtaniyar bayan tarzomar da ta auku.

Shi dai tsohon jami'in 'yan sandan, wato Bill Bratton yana da kwarewa sosai wajen yaki da kungiyoyin matasa dake aikata muggan laifuka a birane kamar Los Angeles, da New York, da kuma Boston.

'Yan sanda kasar sunce ya zuwa yanzu dai a duk fadin Ingila mutane fiye da dubu goma sha shida ne aka kama dangane da tarzomar da ta auku, yayinda an gurfanar da mutane kusan dari takwas a gaban kotu.

Bugu da kari kusan kashi daya bisa biyar na wadanda ake tuhuma basu kai shekara goma sha takwas ba.