Harkokin kiwon lafiya sun tsaya a Syria

Wasu mata masu zanga-zanga a Syria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu mata masu zanga-zanga a Syria

Wani likita a Syria ya bayyana cewa yunkurin murkushe 'yan adawa da jami'an tsaro ke yi ya yi gagarumar illa ga harkokin kiwon lafiya a kasar.

Ya shaidawa BBC cewa jama'a suna kin zuwa manyan asibitoci saboda kasancewar jami'an tsaro, wadanda ake zargin sun kashe wadansu daga cikin wadanda suka jikkata.

Likitan ya kuma ce an lalata asibitoci guda biyu a gumurzun da aka yi na tsawon mako guda, sannan an lalata abubuwa da dama.

A halin da ake ciki kuma, Shugaban Amurka Barack Obama da Sarki Abdullah na Saudi Arebiya sun yi kira ga gwamnatin Syria ta dakatar da amfani da karfi a kan jama'arta.

A wata tattaunawa da suka yi ta wayar tarho, sun nuna matukar damuwa game da halin da ake ciki a kasar ta Syria.

Masu fafutuka a Syria sun ce an kashe akalla mutane tara, yayin da jami'an tsaro suke kokarin dakile zanga-zangar nuna adawa da Shugaba Assad.