An kashe mutane akalla 20 a Afghanistan

Harin kunar bakin wake a Afghanistan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Harin kunar bakin wake a Afghanistan

Mutane akalla ashirin ne suka mutu a sakamakon wani hari a yankin tsakiyar Afghanistan.

Wasu 'yan kunar-bakin-wake ne su su shidda suka kaddamar da hare hare a kan ofishin gwamnan lardin Parwan, inda aka kwashe sa'o'i ana artabu.

Gwamnan, AbdulBasir Salangi na taro ne da wasu jami'an tsaro a lokacin da aka kaddamar da hare haren.

Galibin wadanda suka mutun, fararen hula ne, baya ga wasu jami'an tsaro da kuma daukacin maharan.

Kungiyar Taliban ta ce ita ta kai harin.