'Yar Majalisar Amurka ta yi nasara a kuri'ar jeka-na-yi-ka

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Michele Bachman

'Yar Majalisar Dokokin Amurka daga jam'iyyar Republican kuma mai goyon bayan masu ra'ayin rikau, Michele Bachman, ta lashe kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta farko a yunkurin da wasu 'yan jam'iyyar ke yi na samun damar tsaya mata takarar shugabancin kasa.

'Yan jami'yyar Republican kusan goma sha biyu ne dai ke fafutukar ganin sun samu damar karawa da Shugaba Obama a zaben shugaban kasar da za a gudanar badi.

Misis Bachman ta ce idan ta zama shugabar Amurka, za ta tabbatar da dokokin da za su hana zubar da ciki; da kare hakkin ma'aurata, da na ma'aikata.

Wannan kuri'ar jin ra'ayin, wadda aka gudanar a Iowa, a hukumance ba ta cikin matakan fitar da gwani na jam'iyyar, amma duk da haka alama ce da ke nuna inda ra'ayoyin 'yan jam'iyyar suka fi karkata.