Gwamnatin Libya ta ce ba a kwace garin Zawiya ba

Image caption Moammar Gaddafi

Gwamnatin Libya ta yi watsi da rahotannin da ke cewa 'yan tawaye sun kwace garin Zawiya mai matukar muhimmanci a yammacin kasar.

Wasu 'yan jaridar kasashen duniya wadanda ke tafiya a garin sun ji karar harbin bindigogi, sannan 'yan tawayen suka ba da rahoton cewa dakarun gwamnati sun ranta a na kare.

Sai dai ministan yada labaran gwamnatin ta Libya, Moussa Ibrahim, ya ce garin na karkashin ikon dakarun gwamnati:

''Wasu tsirarun 'yan tawaye ne wadanda ba su kai dari ba suka yi yunkurin nausawa kudu da garin, amma cikin sauki dakarunmu suka taka musu birki''.