'Dalilan da suka sanya 'yan Najeriya ba su amince da 'yan sanda ba'

Image caption 'Yan sandan Najeriya

Wasu 'yan Najeriya sun bayyana cewa halayen 'yan sandan kasar na dorawa mutum laifi babu-gaira-babu-dalili su ne suka sanya ba su saki jiki da su ba.

Wani dan kasar, Alhaji Yakubu, ya shaidawa BBC cewa a yawancin lokuta 'yan sandan na kama mutane ne ba tare da sun aikata wani laifi ba, sannan su kai su wajen da za su kulle su.

Shi ma Mista Dick Sorine ya ce duk da ya ke 'yan sanda na ikirarin cewa za su tabbatar da adalci ga duk mutumin da ya kai musu rahoton masu aikata laifuka, daga karshe reshe ne ya ke juyewa da mujiya.

Ya ce hakan ne ya sanya ba kasafai jama'a kan saki jiki da 'yansanda ba balle ma su kai musu bayanan da 'yan sandan ke bukata don gudanar da ayyukansu.

Sai dai kwamishinan 'yan sanda na jihar Rivers, Sulaiman Abba, ya ce rashin jituwa tsakanin 'yan sanda da jama'a ta samo asali ne tun lokacin Turawan mulkin mallaki inda Turawan ba su damu da yaukaka dangantaka tsakaninsu da jama'a ba.

Sulaiman Abba ya ce babu wata doka da ta yarda da gallazawa jama'a a lokacin gudanar da bincike.