Taron neman zaman lafiya a Birmingham

Kungiyoyin al'umma sun gudanar da wani gangamin neman zaman lafiya a birnin Birmingham na Birtaniya.

Haka na zuwa ne sakamakon tarzomar da aka yi a can cikin makon da ya wuce, a lokacin da aka kashe wasu samari uku, yayinda suke kare shagunansu daga masu kwasar ganima.

Tariq Jahan, mahaifin daya daga cikin matasan da wata karamar mota ta buge, ya shaida wa taron cewar sun mutu ne domin al'umarsu.

An dai tuhumi wasu mutane biyu game da kisan nasu.

Mutuwar mutanen, na daya daga cikin munanan abubuwan da suka faru, a jerin tarzoma , da kwasar dukiyar jama'a, da kuma tayar da gobara a cikin kwanaki da yawa a biranen Ingilar masu dama, musamman a London.

An kama dubban mutane, game da hakan.