An kashe mutane akalla 19 a Latakia

Masu fafutuka a Syria sun ce mutane akalla sha tara ne suka mutu, yayinda dakarun gwamnati suka kaddamar da wani hari ta kasa, da kuma ta ruwa a kan birnin Latakia mai tashar jiragen ruwa.

Sun ce kananan jiragen yaki na ta barin wuta a kan anguwannin jama'a, yayinda kuma tankokin yaki ke rufa masu baya.

Unguwannin dai sun fuskanci manyan zanga zangar neman faduwar Shugaba Assad, sannan kuma dakarun gwamnati sun yi masu kawanya na wani lokaci.

Wasu masu fafutukar sun ce a cikin kwana biyun da suka wuce sun ga karuwar farmakin gwamnati.

Gidan Talabijin mallakar gwamnatin Syriar ya musanta cewar ana kai farmaki ta ruwa.