An kashe mutane da dama a Iraqi

An kashe mutane da dama a Iraqi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hare-haren sun yi barna matuka gaya

Akalla mutane fiye da 60 ne suka rasa rayikansu a sakamakon wasu jerin hare-haren bam da aka kai a wasu garuruwan kasar Iraqi.

A birnin Kut ne al'ammarin ya fi muni inda bama-bamai biyu suka tashi daya bayan daya, tare da hallaka akalla mutane 37.

Sai kuma a garin Khan Bani Sa'ad inda wani dan kunar bakin wake da mota ya kashe akalla mutane goma.

Yayin da wasu 'yan kunar bankin wake biyu kuma su ka kaddamar da wani harin a cibiyar yaki da ta'addanci da ke Tikrit inda 'yan sanda biyu suka rasa rayukansu.

Tattauna makomar sojin Amurka

Wannan tashin hankalin na zuwa ne a daidai lokacin da aka bada labarin wani a Gundumar Diyala, inda mutane 10 suka hallaka.

Makonni biyu da suka wuce, jami'an Iraqi suka ce suna tattaunawa da jami'an Amurka kan yadda dakarun Amurkan za su ci gaba da zama a kasar a shekara ta 2012.

Duka sojojin Amurka za su bar kasar ne a shekara ta 2012, amma jami'an Amurka da na Iraqi sun nuna damuwa kan karfin jami'an tsaron Iraqi na shawo kan matsalar tsaro a kasar.

Yadda ake samu karuwar tashe-tashen hankula a kasar ta Iraki, wata alama ce da ke nuna irin matsalolin da jami'an tsaron kasar za su iya fuskanta idan sojojin kawance suka fice daga kasar.