An kashe mutane bakwai a jihar Plateau

Rahotanni daga jihar Plateau na cewa an samu wani sabon tashin hankali a Haifan, da ke karamar hukumar Barikin Ladi, inda aka ce wasu mutane bakwai dukkaninsu 'yan gida daya suna rasa rayukansu.

Hukumomi a Jihar sun tabbatar da afkuwar wannan lamari, sun kuma ce kawo yanzu suna ci gaba da gudanar da bincike.

Dama dai an wayi garin yau cikin wani zaman zullumi a shi kanshi garin Jos, bayan da aka samu gawar wani dan Achaba da ake zargin hallaka shi aka yi.

Jihar Plateau dai ta yi kaurin suna wajen tashin hankali mai nasaba da kabilanci da kuma addini.