Matakan magance rikice-rikice a Najeriya

Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, jama'a da dama na ci gaba na zayyana hanyoyin da suke ganin su ne za su kai ga tabbatar da samun dawwamammen zaman lafiya tsakanin al'ummomin kasar.

A cewar wasu masana dai tabbatar da adalci ne babbar hanyar samun kwanciyar hankali a Najeriyar.

Dakta Kabiru Mato, wani mai sharhi a kasar, ya ce almundahana da shugabanni ke yi da kudaden jama'a ne ke kawo yawan rikici a kasar.

Ya ce dole ne shugabanni su daina sace kudaden jama'a idan ana son samun zaman lafiya.

Shi ma Malam Muhammad Bin Uthman, wani malamin addinin Musulinci, ya ce ya kamata shugabanni su rika yin adalci don magance yawan rikice-rikice a kasar.