Za a gurfanar da Amurka a gaban kuliya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Amurka, Barack Obama

Wadansu kamfanoni yin taba sigari za su kai gwamnatin Amurka kara a kan wata doka wadda za ta tilasta su rubuta gargadin yiwuwar kamuwa da cuta baro-baro a jikin kwalin sigarin na su.

Kamfanonin sun ce ka'idar ta yi karan tsaye ga 'yancin da kundin tsarin mulkin kasar ya ba su ya bayyana albarkacin bakinsu, tun da ta wajabtawa kamfanonin yada sakwannin gwamnati na yaki da shan taba sigari.

A karkashin dokar, wadda hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka ta tsara, daga karshen badi wajibi ne a lika sakwannin gargadi ciki har da hotunan rubabun hakora da hunhun mara lafiya don jawo hanaklin masu busa sigari su daina.

Kamfanonin na so ne a bayyana wannan doka da cewa ta sabawa kundin tsarin mulki.