'Hauhawar farashi za ta jefa mutane cikin hatsari'

Image caption Tambarin Bankin Duniya

Bankin Duniya ya ce hauhawar farashin kayayyakin abinci na jefa al'ummar da ke matalautan kasashe cikin hadari, kuma yana kara ta'azzara matsalar yunwa da fari a Kusurwar Afirka.

Wani masanin kasuwancin amfanin gona wanda ke aiki da wata kungiyar farar hula a arewacin Kenya, George Mukkath, ya ce al'amura za su inganta ne kawai idan aka kara zuba jari a bangaren aikin gona:

'' Za mu ci gaba da ganin yanayi na fari a ko wanne lokaci, kuma muddin ba a zuba jari sosai a bangaren aikin gona ba, to za a ga mummunan sakamako''.

A rahotonsa na baya-bayan nan, Bankin Duniyar ya ce ko da yake farashin kayan abinci ya sauka bayan da ya yi tashin gwauron zabi a watan Fabrairu, har yanzu ya haura yadda ya ke a bara da kashi daya bisa uku.

Farashin kayan abinci kamar masara ya tashi da kashi tamanin da hudu cikin dari yayin da na alkama ya tashi da kashi hamsin da biyar cikin dari.