An kame daruruwan masu fafutuka a India

Anna Hazare Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Anna Hazare ya sha alwashin gudanar da azumi domin korafi kan cin hanci

'Yansanda a Indiya sun kama masu fafutukar yaki da cin hacni 1,300 a daidai lokacin da suke shirin fara yajin aikin cin abinci.

Shaharran dan fafutukar nan Anna Hazare, an kama shi a gidansa sa'o'i kadan kafin ya fara azumi na ko a mutu ko a yi rai tare da magoya bayansa su dubu biyar a wani filin wasan kurket.

Sun shirya yin hakan ne dai domin nuna damuwa kan wata sabuwar dokar yaki da cin hanci da rashawa.

Kafofin yada labarai na kasar sun ba da rahoton an kama Mista Hazare ne don tabbatar da bin doka ada oda a babban birnin kasar ta India.

A ranar Litinin 'yansanda suka ki ba Mista Hazare izinin gudanar da ganagamin da ya ke shirin yi.

Fira Ministan kasar Manmohang singh ya sha alwashan tunkarar matsalar cin hanci da rashawa, sannan kuma ya ce gangami da yajin cin abinci ba za su taimaka wajen magance matsalar ba.

Hukumomi a kasar sun ce an kame masu fafutukar ne saboda sun sabawa ka'idojin da 'yansanda suka basu na gudanar da zanga-zangar.