'Yan sanda sun kama dan fafutuka a India

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Anna Hazare

'Yan sanda a Indiya sun kama wani mai fafutukar yaki da cin hanci da rashawa a gidansa da ke Delhi.

Mai fafutukar, Anna Hazare, ya shirya yin azumi ne na ko a mutu ko a yi rai tare da magoya bayansa su dubu biyar a wani filin wasan kurket da nufin tilastawa gwamnatin kasar ta dauki matakin magance cin hanci da rashawa.

Kafofin yada labarai na kasar sun ba da rahoton dake cewa an kama Mista Hazare ne don tabbatar da bin doka ada oda a babban birnin kasar ta Indiya.

Jiya Litinin 'yansanda suka ki ba Mista Hazare izinin gudanar da gangamin da ya ke shirin yi.