Mahukunta sun ce a saki Anna Hazari a Indiya

Anna Hazare Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Anna Hazare ya sha alwashin gudanar da azumi domin korafi kan cin hanci

Mahukunta a Indiya sun bada umarnin a saki gogaggen mai fafitikar yaki da cin hanci da rashawa, Anna Hazare, 'yan sa'o'i bayan da aka gudanar da jerin zanga-zanga a kasar, sakamakon kama shi da hukumomin kasar suka yi.

Sai dai rahotannin sun ce ya ki amincewa da tayin hukumomin na sakin na shi.

An dai daure shi na tsawon mako daya, bayan da ya ce zai fara wani yajin cin abinci don nuna fushinsa da gwamnati saboda ta gaza daukan kwararan matakai na yaki da matsalar ta cin hanci da rashawa a kasar.

Amma gwamnati ta ce yajin cin abincin na yin barazana ga doka da oda.

Zanga-zanga ta bazama

'Yan adawa a kasar ta India dai sun yi Allah Wadai da kamun Mr Hazare din, kuma an tsare dubban magoya bayansa a duk fadin kasar.

Mr Hazare dai ya ce ya kamata Hukumar da gwamnati za ta kafa don yaki da cin hanci da rashawa, ta samu ikon bincikar duk wani jami'in gwamnati, ciki har da Fira minista da kuma alkalai.

An dai kame shi ne a daidai lokacin da daruruwan magoya bayansa suka kewaye motar 'yan sandan da aka yi amfani da ita wajen yin awon gaba da shi suna kada tutoci suna kururuwa:

Daga bisani dubun dubatar magoya bayansa sun hau kan tituna suna zanga-zanga a duka fadin kasar.

'Kada ku bari hakan ta kasance'

A birnin Delhi, magoya bayansa sun taru a dandalin tunawa da Mahtma Ghandi, a dai-dai lokacin da ake tsuga ruwan sama suna rera wake-wake:

Daga bisani 'yan sanda sun yi awon gaba da da dama daga cikinsu.

Shi dai Mr Anna Hazare, wanda mai fafatukar kare al'umma ne, ya shirya gudanar da yajin cin abinci ne a bainar jama'a har ya mutu tare dubban magoya bayansa a wani filin wasa na kurket domin tilasta wa gwamnati ta dau mataki kan karuwar cin hanci da rashawa a kasar.

'Yan sanda sun hana shi izinin gudanar da taron yajin cin abincin. Ya kuma ce kama shin da aka yi ba zai kawo karshen yekuwar da yake yi ba:

"A yanzu an fara gwagwarmayar kwatar 'yanci karo na biyu. Kuma ni ma an kama ni. Shin kama ni zai kawo karshen gwagwarmayar? Sam hakan ba za ta yiwu ba, kuma kada ku bari hakan ta kasance".

Ministocin gwamnati sun kare matakin kame Azarin da magoya bayansa da cewa Mr Azare na barazana ga zaman lafiyar al'umma saboda gangamin da ya shirya.