Tarayyar Turai na neman tsarin tattalin arziki na bai daya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sarkozy da Merkel

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy sun fitar da wasu matakai na karfafa kudin Euro tare kuma da yunkurin kawo karshen matsalar bashin dake addabar kasashen dake amfani da kudin na Euro. Shugabannin a ganawarsu a birnin Paris na kasar faransa, sun amince da karin hadin kan siyasa da kuma kafa gwamnatin bai daya da zata duba batun tattalin arzikin su. Nicholas Sarkozy kenan yake cewa na farko a tsare tsaren ya hada da kafa hukumar da zata sa ido akan tattalin arzikin kasashen dake amfani da kudin Euro. Hukumar za ta kunshi masu bada shawara ga shugabannin kasashen. Za kuma su dinga ganawa sau biyu a duk shekara idan bukatar hakan ta taso.