Za a sake yiwa James Murdoch tambayoyi

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption James Murdoch

Wani mamban majalisar dokokin Burtaniya ya ce mai yiwuwa a sake yin tambayoyi ga dan Rupert Murdoch, James.

Kwamitin majalisar da ke bincike game da satar sauraren wayar jama'a da ake zargin jaridar News of the World ya yi dai ya samu sabbin hujjoji, kuma shugabansa John Wittingdale, ya shaidawa BBC cewa akwai bambance-bambance a bayanan da wadanda abin ya shafa suka gabatar.

Kwamitin ya wallafa wata wasika wacce ta fito daga tsohon wakilin jaridar a fadar Sarauniyar Ingila, Clive Goodman, wanda aka daure saboda laifin satar bayanai.

A cikin wasikar tasa, Mista Godman ya yi zargin cewa manyan jami'an jaridar na da masaniya game da satar bayanan da ake yi.