Jonathan ya rantsar da Ngozi Okonjo-Iweala

Ngozi Okonjo-Iweala Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana saran za ta bullo da sauye-sauye a fannin tattalin arzikin kasar

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya rantsar da tsohuwar manajar darakta a bankin duniya Ngozi Okonjo-Iweala, a matsayin ministar kudi ta kasar.

Rantsuwar tata ta zo ne wata guda bayan rantsar da takwarorinta na majalisar ministocin kasar.

"Jama'a za su yi mamaki mai ya sa muka dawo da ke bayan kin rike wannan mukami a baya. Muna bukatar ki taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasarmu," a cewar Jonathan jim kadan bayan ya rantsar da ita.

Masu zuba jari na sa ido sosai kan irin matakan da za ta dauka, da kuma yadda za ta yi aiki tare da shugaban babban bankin kasar Sanusi Lamido Sanusi.

Mr Sanusi ya bullo da sauye-sauye da dama a fannin bankunan kasar, abin da ya kai ga gwamnati saye wasu daga cikin bankunan da suka gaza ka'idojin da aka shimfida musu.

Ngozi ta taba zamowa ministar kudi a Najeriya lokacin shugaba Olesegun Obasanjo, kafin daga bisani ta koma bankin duniya domin ci gaba da aiki.