Najeriya ta sake kaddamar da tauraron dan Adam

Image caption Taswirar Najeriya

Najeriya ta kaddamar da sabbin na'urorin tauraron dan Adam guda biyu, wato Nigeriasat-x da kuma Nigeriasat-2, a kasar Rasha.

Masana kimiyya daga Najeriya ne suka kirkiri Nigeriasat-x, yayin da kuma aka kirkiri Nigeriasat-2, tare da hadin gwiwar kamfanin Surrey Satellite Technology na Burtaniya.

"Ina taya jama'ar kasarmu murna, ganin yadda muka fara nisa a kokarinmu na dogaro da kai a fannin kimiyya da fasaha," a cewar Shugaba Goodluck Jonathan. "A yanzu da muke da wadannan na'urori a sararin samaniya, ina kira ga ma'aikatan gwamnati da kuma kamfanoni masu zaman kansu da su yi amfani da damar da wadannan na'urori za su samar".

Shugaban Hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya Sa'idu Mohammed, ya shaida wa wa BBC cewa za a yi amfani da taurarin dan Adam din ne wajen bunkasa aikin gona, da samar da tsaro, da dai makamantansu.