Rasha ta cika shekaru 20 da kafuwa

Rasha ta cika shekaru 20 da kafuwa
Image caption Shugabannin wasu tsaffin kasashen Tarayyar Soviet na sa hannun kan yarjejeniyar samun 'yancin kai

A ranar Juma'a ne kasar Russia ke cika shekaru ashirin tun bayan juyin mulkin ranar 19 ga watan Agusta na shekarar 1991, wanda ya yi sanadiyyar rugujewar Tarayyar Soviet.

Juyin mulki wanda aka yi saboda tsare-tsaren kawo sauyin da Shugaban Tarayyar Soviet na karshe wato Mikhail Gorbachev ke shirin yi, ya janyo durkushewar Tarayyar Soviet din a watan Disambar wannan shekarar.

Kasashe 15 da suka hadu suka yi Tarayyar abaya suka zamo kasashe masu 'yancin kansu.

Sun kuma kirkiro sauye-sauyen tattalin arziki da siyasa, amma sauye-sauyen ba su yi tasiri ba, domin rayuwar jama'a ta ci gaba da kasancewa cikin koma baya. Bikin ranar cikar shekaru ashirin din dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun yanayi na rashin tabbaci kan wanda zai shugabanci kasar ta Russia a shekaru shida masu zuwa.

An dora alhaki kan Mikhail Gorbachev

Durkushewar Tarayyar Soviet shi ne ya kawo karshen cece-kuce da rarrabuwar kai a tsare-tsaren siyasar kasar da kuma gwamnatin tsakiya ta Tarayyar Soviet Socialist Republics.

An dora alhakin durkushewar Tarayyar Soviet din ne akan gazawar da Mikhail Gorbachev wato shugaban Tarayyar Soviet daga watan Maris na shekarar 1985 ya yi, na kasa daukar matakan farfado da tattalin arziki ta wata takaitacciyar hanyar sassaucin siyasa bisa tsarin Kwaminisanci na jam'iyya guda a kasar.

Image caption Wasu daga cikin mutanen da 'yan Chechnya suka yi garkuwa da su Budennovsk

Rashin zaman lafiya a Tarayyar ya karu a saboda ci gaba da bunkasa sojin Soviet maimakon ayyukan ci gaban cikin gida da kuma tsayawa cik da tattalin arziki ya yi.

Yanayin tattalin arzikin ya kai makura, sannan kuma duk wani yunkurin yin gyara akansa ya ci tura.

Gibin cinikayyar Tarayyar Soviet ya taimaka wajen karayar tattalin arzikinta.

Rasha ce ta gaji Tarayyar

Komai ya bayyana a zahiri sakamakon faduwar farashin danyan mai a shekarar 1985, wanda kuma zabin karshe da ya ragewa shugaban Tarayyar Soviet na wancan lokacin Mikhail Gorbachev shi ne ya bada karin 'yanci na siyasa da zamantakewa wanda ya bada kofar kalubalantar gwamnatin kwaminisancin karara.

Yakin da aka yi a kasar Afghanistan wanda ake wa lakabi da yakin Vietnam na Tarayyar Soviet, shi ne ya sake janyo kyamata da kuma sanyayawa sojin Soviet din gwuiwa.

Abinda ya janyo durkushewar Tarayyar Soviet din kacokam shi ne lokacin da suka janye daga Afghanistan a saboda tunanin Gorbachev na bullo da sauye-sauye a manufofinta na kasashen waje da na cikin gida.

A shekarar 1991 ne dai Tarayyar Soviet ta wargaje baki daya inda Boris Yeltsin ya karbe iko, bayan wani yunkurin juyin mulkin da aka yi da ya so tumbuke Gorbachev mai yunkurin kawo sauyi.

Kasar Rasha ce dai a yanzu ke a matsayin wadda ta maye gurbin tsohuwar Tarayyar ta Soviet.

Shekaru da dama bayan durkushewar tarayyar Soviet, wadda aka kafa a shekarar 1922, yankin ya ci gaba da kasancewa wani jigo a siyasar duniya.

Karin bayani