Mutane da yawa sun mutu ko jikkata a harin Isra'ila

Tutar Isra'ila
Image caption Tutar Isra'ila

Wasu 'yan bindiga da ba a shaida ba, sun kai wasu jerin hare hare a Kudancin Isra'ila, inda suka kashe mutane da dama, suka kuma raunata wasu masu yawa, a kusa da kan iyaka da Masar.

Laftanar Kanar Avital Leibovitch , kakakin sojin Isra'ilar;ta ce, "an yi barin wuta mai zafin gaske a kan wannan motar bus. An raunata mutane masu yawa a harin."

Baya ga motar bus ta farko, kafafen yada labaran Isra'ila sun ce an kai harin bam a kan wata ta biyu.

Dakarun Isra'ila sun yi arangama da 'yan bindigar a kusa da inda aka kai hari na farko, inda suka kashe biyu daga cikinsu.

Wani likita ya ce an kwantar da mutane ashirin da biyar a asibitinsa, galibin su sojoji.