Za'a kaddamar da majalisar tattalin arzikin Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

A ranar Alhamis ne ake saran shugaban kasar Najeriya zai kaddamar da wani kwamiti na musamman akan tattalin arzikin kasar.

Kwamitin wanda ya kunshi mambobi ashirin da hudu, zai kasance ne karkashin jagoranci shugaban kasar.

Sai dai tuni Masana harkar tattalin arziki a Najeriya suka fara fashin baki akan kwamitin, da kuma irin rawar da suke ganin kwamitin zai taka wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriyar.

Malam Yusha'u Aliyu wani masanin tattalin arziki a Abuja ya shaidawa BBC cewa kwamitin zai yi tasiri saboda zai yi kokarin shawo kan banbance banbancen da ake dasu a tsarin tattalin arzikin kasar.