Syria ta ce ta dakatar da matakan soji kan 'yan adawa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Bashar Al Assad

Shugaban kasar Syria, Bashar al-Assad, ya shaidawa sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya cewa, ya dakatar da daukar matakan soji kan masu adawa da gwamnatinsa.

Mr Assad ya baiwa Ban Ki Moon wannan tabbaci ne a ganawar da suka yi ta wayar tarho.

Gidan talabijin na Syria ya nuna tankokin yaki da dakarun soji na janyewa daga birane.

Sai dai yan adawar, sun ce har yanzu ana halaka masu zanga zanga kuma an kashe kimanin mutane ashirin a jiya laraba.

Wakilin BBC ya ce ya kamata a nuna shakku a kan kalaman Mr Assad yayinda sojojin kasar na cikin jami'an tsaro goma sha bakwai da ake amfani dasu wurin murkushe masu zanga zanga.